BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Tarihin Harkar Musulunci A
Nigeria
Harkar Musulunci karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky ta tsiro ne tun kafin cin nasarar juyin juya hali na kasar Iran, watau tun lokacin shi Sheikh din yana dan makaranta a jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria.
Sai dai a hankali ne harkar ta rika daukan siffa yayin da su yan uwa na harkar suke kara yawa kuma suke kara samun tarbiyya da ilmi na addinin musulunci.
Daga cikin irin ayyukan tarbiyya da harkar ta dauka akwai irin su
karantarwa da ake kira
Ta'alim,Ijtima, Daura,Ribat...
TA'ALIM
Wannan wani dandali ne na
karantarwa da ake yi mafi
yawa a masallatai na
unguwowi daban daban na
garuruwan da yanuwa din
suke. Akan sa rana guda ne ko
biyu gwargwadon yadda zai
zama daidai da zarafin su yan
uwa din inda ake taruwa maza
da mata tare da jagorancin
wakilin wannan gari inda za'a
karanta hadisai da ayoyi na
tarbiyyar dabi'u da ruhi don
kara samun kusanci da Allah
tabaraka wa ta'ala. Baya ga
wannan ta'alim na kowa da
kowa kuma kawai wani na
daban wanda mafi yawa ake yi
tsakanin wasu zababbu daga
cikin yan uwa don karantarwa
ta musamman ta yadda su
wadannan yan uwa sun
kasance sun fi sauran fadin ilmi
da fahimta da dai sauransu.
IJTIMAH
Wannan ma wani bangare ne
na ayyukan da aka sa agaba a
harkan domin ganin an inganta
tarbiyyan yanuwa koda yake ita
ijtimah ta kasance tun a farko-
farkon kafuwan harkan inda
ake taruwa a daya daga
masallatan jummu'a na
garuruwan Kano da Zaria
domin gudanar da manyan
ijtima'oi ko kuma masallatan
jummu'a na garuruwa daban
daban don gudanar da
kananan ijtimao'i. Daga baya
bayan da harakr ta kara
bunkasa sai ya zamana
wannan nauin tarbiyyar ba zai
yiwu ba saboda dalilai masu
yawa ciki har da yawan jama'a
don haka sai aka koma yin
"Daura" maimakon ijtimah.
DAURA
Kamar yadda muka ambata a
sama "Daura" ce ta maye
gurbin ijtimah bayan da
matsayin ijtimah din ya zama
ba mai yiwuwa ba. Yadda aka
saba gudanar da wannan abu
kuwa shine ta hanyar shirya
jawabai na malamai tare da
mauduai daban daban da suka
shafi tunani watau kyautata
fikra kyautata dabi'au gayaran
ruhi da dai sauran su wanda
ake yi da manufar budawa
yanuwa hanyar gyaran kai na
tsawon kimanin kwanaki
kamar bakwai watau sati daya.
Mafi yawa a karshen ko wacce
daura akan rufe ne tare da
jawabin jagoran harkan Mallam
Ibrahim Zakzaky. Galibi wannan
daura kan banbanta da
Mu'tamar wanda ake gabatar
da shi ta hanyar gayyatan
sauran musulmi na gari kowa
da kowa kuma galbi yakan fi
yawan jama'a.
MU'UTAMA
Kamar yadda muka ambata
wannan shima wata hanya ce
ta haduwan yanuwa da kuma
bayar da tarbiyya domin akan
hadu ne a daya daga cikin
dakunan taro na zamani ko
daya daga cikin masallatai na
gari don gudanar da shi. Inda
ake gayyatar Malamai daga
bangarori daban na kasar don
gabatar da laccocin su akan
mauduai daban daban don
kyautata tarbiyyar juna. Shima a
mafi yawan lokutta ana rufewa
ne tare da jawabin jagoran
harkar Mallam Ibrahim Zakzaky.
WA'AZOZIN RANAKUN JUMMA'A
Wa'azozin ranakun jummu'a na
daya daga cikin manyan
ayyukan wannan harkar inda
ake samun haduwa da jama'ar
musulmi a garuruwan daban
daban don bijirar da matsaloli
na duniya da kuma musamman
ma abin da yake damun
musulmi a wannan lokacin
saboda samun karin haske kan
abin da kuma shiray tunanin
musulmi din don ingantacciyar
mafihimta game da yanayi da
kuma siyasar dake cikin irin
wannan abu. Haka nan kuma ta
wannan hanya ana samun yin
magana kan al'amurran da
suke bijirowa kamar irin su
lokutan watannin azumi, Hajj,
da dai sauran watanni na ibada
na musulmi, don karin haske
kan irin abin da suka doru
akan al'ummar musulmi na
farilla da mustahabbai.
Babu shakka a wasu masallatai
da ya zamana ba zai yiwu a
aiwatar da wannan abu kafin
huduba ba ana samu ne a
aiwatar bayan salla jumma'a
kafin mutane su watse su nufi
gidajen su.
BUKUKUWA DA RANAKUN JUYAYI
Daga cikin abin da yanuwa
suka sa a gaba akwai tunawa
da ranakun farin ciki da kuma
na bakin ciki watau bukukuwa
da kuma juyayi na
munasabobin ma'asumai da
magabata don yin nazari kan
rayuwarsu mai albarka da
kuma daukan darasi a cikin
rayuwar mu ta yau da kullum.
Shima wannan wasu lokuta
ana yin su ne ta hanyar wakilan
wannan harka din a garuruwa
daban daban ko kuam ta
jagoran hakar Mallam Ibrahim
Zakzaky. Cikin irin ranakun da
ake gabatar bukukuwa don
tunawa da su akwai kamar su
ranar 17 ga watan Rabiul
Awwal watau ranar haihuwar
fiyayyen halitta Manzon Allah
[SAWA], 15 ga watan Sha'aban
watau daidai da ranar da aka
haifi Sahibuzzaman Imam
Mahdi[AS], ranar haihuwar
sauran a'imma da dai sauran
bayin Allah na gargaru.
Ranakun juyayi sun hada da
ranar wafatin Manzon Allah
[SAWA], ranar shahadar Imam
Hussain[AS] a Karbala... da dai
sauransu.
MUZAHARORI
Muzaharori ko kuma jerin
gwano na daya daga cikin
hanyar da wannan harka ke bi
saboda bayyana abu muhimmi
daya shafi al'ummar musulmi
kamar ranakun Qudus wanda
akae gabatar da jerin gwano
na gaba dayan kasar sannan
kuma ko wanne gari su
gabatar nasu na daban don
nuna goyon baya ga al'ummar
Palasdinawa da kuma yin tofin
Allah ya tsine ga su
haramtacciyar kasar Isra'ila kan
irin ta'addancin da take
tafkawa a yankin na Palasdin.
Koda yake dai a mafi yawan
lokaci ana kokarin gabatar da
wannan muzahara ta ruwan
sanyi amma lokuta da dama
ana samun matsalar kawo hari
daga bangaren yan sanada da
jami'an tsaro.